Kasar Sin ta janye rangwamen haraji da ta yi wa kayayyaki 128 da Amurka ke shigarwa kasar daga yau Litinin, ciki har da naman alade da kayan marmari
Wata sanarwar da hukumar kula da harajin kayakin da ake shigo da su ta majalisar gudanarwar kasar ta wallafa a shafinta na Intanet ta ce, ta yanke shawarar sanya harajin kaso 15 kan kayaki 120 da Amurka ke shigo da su, ciki har da kayan marmari da dangoginsu, da kuma kaso 25 kan kayaki 8 ciki har da naman alade da dangoginsa.
Sanawar ta ruwaito cewa an dauki matakin ne domin mayar da martani ga matakin Amurka na sanya haraji kan kayakin karafa da goran ruwa da ake shigar da su kasar.
Duk da adawar da kasashen duniya suka nuna game da matakin, gwamnatin Amurka ta yanke shawarar sanya haraji da kaso 25 kan karafa da kuma kaso 10 kan gorar ruwa, tare da wasu harajin kan kayakin da wasu kasashe ke shigarwa kasar, ciki har da Kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)