Jiya Laraba jakadan kasar Sin da ke kasar Amurka Cui Tiankai, ya gana da mukaddashin sakataren harkokin wajen kasar Amurka John J. Sullivan a birnin Washington DC., inda suka yi musayar ra'ayoyi kan huldar da ke tsakanin kasashen 2, da sauran batutuwa.
A yayin ganawar tasu, mista Cui Tiankai, ya sake nanata matsayin kasar Sin dangane da batun tattalin arziki da ciniki a tsakaninta da Amurka. Ya kuma bukaci Amurka da ta yi watsi da ra'ayin kashin kai, da matakin ba da kariya kan harkokin ciniki cikin hanzari, ta kuma sa aya ga bincike mai lamba 301 da take yi kan kasar Sin, kana ta hada kai da kasar Sin wajen daidaita wannan sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa. (Tasallah Yuan)