Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron manema labaru a yau Laraba a nan Beijing cewa, babu wanda zai ci nasara bisa matsalar ciniki da ta kunno kai tsakanin Sin da Amurka. Ya ce duk wanda ya haddasa matsalar ciniki zai hadu da illar da matsalar za ta haddasa, tare da raunana moriyar sauran sassa. Don haka kasar Sin na fatan Amurka za ta dakatar da matakan kashin-kai, da kuma ba da kariya ga cinikayya. Za kuma ta koma tattaunawa, da yin hadin gwiwa domin samun moriyar juna.
A ranar 3 ga wata, bisa agogon gabashin kasar Amurka, ofishin wakilin Amurka kan harkokin ciniki, ya kaddamar da takardar sunayen kayayyaki da ya shawarci a kara dorawa haraji, bisa ga sakamakon bincike mai lamba 301. (Tasallah Yuan)