A yau Laraba ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ta bayyana cewa kasar ta gabatar da bukatar tattaunawa karkashin tsarin kungiyar ciniki ta duniya wato WTO, dangane da shawarar dora haraji da kasar Amurka za ta yi kan wasu kayayyakin da kasar Sin take sayarwa a Amurka, bisa sakamakon bincike lamba mai 301, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta kadddamar da matakin daidaita matsalar ciniki karkashin tsarin WTO a hukumance. Har ila yau, kasar Sin na fata da kuma imanin cewa, sashen daidaita matsala karkashin shugabancin kungiyar WTO, zai daidaita lamarin cikin adalci kuma bisa sanin ya kamata, zai kuma kiyaye tsarin ciniki na kasa da kasa, inda ake mayar da ka'idoji a matsayin jigo. (Tasallah Yuan)