in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ja hankalin Amurka game da yunkurin baiwa kasuwa kariya
2018-03-30 20:37:14 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana bukatar kasar Sin ga mahukuntan Amurka, da su yi duba na tsanaki game da aniyar su ta baiwa kasuwannin Amurkar kariya.

Lu Kang ya yi wannan tsokaci ne, yayin taron manema labarai na rana rana da ake gudanarwa. Jami'in na wannan tsokaci ne a matsayin martani ga kalaman jakadan Amurka a kasar Sin Terry Branstad, wanda ya ce akwai yiwuwar Sin ta yi ramuwar gayya ta hanyar sanya haraji kan waken soya da take sayowa daga Amurka.

Mr. Lu ya ce ba wai sashen masu sarrafa kayan amfanin gona na Amurka ne kadai ke nuna damuwa, game da yiyuwar tabarbarewar alaka tsakanin kasashen biyu, biyowa bayan matakan da Amurkar ke dauka ba.

Don haka dai Sin ke fatan bangaren Amurka zai amince da shawarar masu sayayya na Amurka, da 'yan kasuwa da sauran al'ummar ta.

Ya ce, "mun dade muna maimaita cewa Sin ba ta son yakin cinikayya". Sai dai kuma Lu Kang ya ce idan har aka tilasa mata shigar sa, Sin na da kwarin gwiwa da ikon tunkarar kalubalen dake tattare da hakan.

Daga nan sai ya kara da cewa, muddin aka shiga irin wannan yaki na cinikayya, bangaren da aka matsawa ne zai yanke shawara game da lokaci da yanayi, da kuma sassan da zai maida martani a kan su gwargwadon bukatar sa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China