Li Zhanshu ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tana da babbar ma'ana ga kasashen biyu, har ma ga kasa da kasa gaba daya. Ana fatan kasashen biyu za su daidaita dangantakar dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, da kara cudanya da juna, da hadin gwiwa da juna, da daidaita matsalarsu yadda ya kamata, don tabbatar da raya dangantakar dake tsakaninsu. Har ila yau majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na fatan amfani da tsarin mu'amala tare da majalisar dokokin kasar Amurka, wajen girmama moriyar juna da batutuwan da suke lura da su, da sa kaimi ga hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, a kokarin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, Mr. Daines ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin tana da muhimmanci sosai, yana kuma fatan za a ci gaba da kokari wajen sa kaimi ga samun amincewa, da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu. (Zainab)