Tada takaddamar ciniki da Amurka ta yi abu ne da bai dace ba, in ji jami'in Benin
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wata takardar bayani kwanan baya, inda ya ce, bisa rahoton bincike na sashe na 301 da aka fitar, kasarsa za ta sanya gagarumin haraji kan kayan da take shigowa da su daga kasar Sin, da kuma takaita ayyukan zuba jari gami da sayen kamfanonin Amurka da kamfanonin Sin za su yi. Game da wannan batu, mataimakin shugaban hukumar bunkasa harkokin fitar da kayayyaki zuwa ketare da zuba jari gami da kasuwanci na Jamhuriyar Benin, Gaetan Kouponou ya bayyana cewa, ya kamata Amurka ta yi la'akari da ra'ayin kasashen dake tasowa gami da ra'ayoyinsu, kana, abun da Amurka ta yi, sam bai dace ba.
Gaetan Kouponou ya kara da cewa, takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka za ta yi illa ga sauran kasashen duniya, ciki har da kasashen Afirka. Masu hikimar sun yi magana cewa, idan giwaye suka yi fada, ciyayin kasa ne za su dandana kudarsu. Wannan ya nuna cewa, kila kasashen Afirka za su fuskanci mawuyacin hali sakamakon takaddamar tsakanin manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.
Har wa yau, Gaetan Kouponou ya ce, kasar Sin ta dade tana la'akari sosai da babbar moriyar kasashen Afirka gami da abun da suke so su yi, kana, Benin ta yabawa kasar Sin saboda hikimar da take nunawa yayin da take daidaita harkokin duniya.(Murtala Zhang)