A yayin taron mambobin kungiyar, Mr. Azevedo ya bayyana ra'ayinsa kan jawabin da Amurka da wasu mambobin kasashen kungiyar suka yi game da matakan cinikayya da suka dauka. Ya ce, matakan da suka dauka sun nuna cewa, a halin yanzu, ana fuskantar kalubalen karuwar shingen cinikayya a fadin duniya, inda ya ce ya kamata a mai da hankali kan batun.
A ranar 1 ga watan nan ne, shugaban kasar Amurka ya sanar da cewa, kasarsa za ta fidda wani mataki a makon nan da muke ciki, inda za ta kara kudin haraji na kashi 25 bisa dari a fannin shigar da karfa, yayin da za ta kara haraji da kashi 10 bisa dari a fannin shigar da hajojin langa samholo.
Matakin na Amurka ya sha suka daga bangarori daban daban. (Maryam)