Darakta janar na kungiyar WTO, Roberto Azevedo, ya bayyana taron na WTO wanda ya samu halartar mambobi 164 da cewar abin takaici ne, sai dai yace an dan samu cigaba.
Azevedo, ya amince cewa, babu wani takamamman sakamako da aka samu a fannin aikin gona, wanda shine babban jigon da taron na kasar Argentina ya mayar da hankali kansa.
Kimanin shawarwari 20 ne aka gabatar wadanda ake ganin zasu iya yin tasiri wajen saukaka fannin aikin gona da kuma wasu matakai da ake ganin sun kasance a matsayin ababen dake haifar da tarnaki wajen aiwatar da tsarin ciniki cikin 'yanci, amma babu koda guda da aka amince da shi.
"Dole ne bangarori su nuna sauye sauye. Ba lallai ne ka samu dukkan abubuwan da kake so ba, amma kuma ba zai yiwu ka janye jiki a dena damawa da kai ba" inji Azevedo, a lokacin da ake yada jita jitar cewa Amurka ta riga ta dauki mataki mai tsauri a lokacin tafka mahawarar game da irin alkiblar da WTO ya kamata ta bi.