Wasu mansanan tattalin arziki su hudu daga kasashen Amurka, Sin da Australia sun bayyana a wata takardar da hukumar binciken alkaluman tattalin arziki (NBER) ta fitar a karshen watabn Yuni cewa, irin babban tasirin cigaban da kasar Sin ta haifar a duniya baki daya a bayyane yake, kuma fanni ne da ake cigaba da yin nazari kansa.
Bayanan binciken sun nuna cewa, tun lokacin da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO ta yi sanadiyyar saukar farashin kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa a Amurka da kashi 7.6 cikin 100, tsakanin shekarun 2000 da 2006. (Ahmad)