A jawabinsa na bude taron, Darakta Janar na hukumar Roberto Azevedo, ya ce kara bude kofa da saukaka hanyoyin cinikayya za su kara bada dimbin damarmakin cimma nasara.
A nasa jawabin, shugaban Argentina Mauricio Macri, kira ya yi ga mambobin hukumar su inganata tsarin tabbatar da adalci da kasuwancin tsakanin kasa da kasa da bisa ka'idoji masu sauki.
Taron wanda zai kai har Laraba ana yinsa, zai hada jami' an harkokin cinikayya daga kasashe mambobin hukumar 164, inda za su tattauna kan yadda za a yi inganta ka'idojin cinikayya a duniya. (Fa'iza Mustapha)