in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mambobin WTO sun bukaci a hada kai domin kare tsarin kasuwanci na hadin gwiwa
2017-07-27 11:43:57 cri
Mambobin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, sun bukaci a hada kai domin kare tsarin kasuwanci na hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki.

Mambobin kungiyar 47 sun fitar da wata takardar sanarwa ta hadin gwiwa a jiya Laraba, wadda ke kunshe da kudurin neman hadin kan juna, ta yadda za a kai ga dakile kalubalen da kungiyar ke fuskanta a wannan fanni.

Sanarwar mai kunshe da sa hannu wakilan kasashen Australia, da Canada, da Sin, da Rasha, da Singapore da dai sauran su, ta tabbatar da cewa kungiyar na fuskantar matsaloli da dama, wadanda ya zama wajibi a dage domin shawo kan su.

Wakilan kasashen na WTO sun kara da cewa, ya zuwa yanzu, akwai karancin himma da hadin kai daga masu ruwa da tsaki, game da burin tattaunawa, ta yadda za a kai ga shawo kan wadannan matsaloli.

Hakan dai na zuwa ne gabanin bude taro na 11, na ministocin kasashe mambobin kungiyar da ke tafe a watan Disambar bana a birnin Buenos.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China