Cikin rahoton da hukumar ta fitar a jiya, babban darektanta Roberto Azevedo, ya yi bayanin cewa, idan masu tsara manufofi sun dauki tsauraran matakai na kayyade shigar da kayayyaki domin samar da guraben aikin yi a kasashensu, lallai harkokin cinikayya ba za su taimakawa bunkasar tattalin arziki ba, inda ya ce zai iya yi wa farfadowar tattalin arziki tarnaki.
A don haka, ya yi kira ga gwamnatocin kasa da kasa, da su inganta aikin samar da ilimi da bada horo, don yin amfani da harkokin cinikayya wajen kara samar da guraben aikin yi. (Lubabatu)