A yayin taron, Zhong Shan ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana ra'ayoyi guda hudu, wadanda suka hada da, na farko, kawar da talauci a matsayin muhimmin nauyin dake wuyan gamayyar kasa da kasa, sabo da haka, kasar Sin ta yi kira ga mambobin kungiyar WTO da su yi hadin gwiwa domin aiwatar da jadawalin neman dawwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030 na MDD. Ya kamata a mai da hankali kan kasashe mafi fama da talauci da kuma al'ummomi mafi fama da talauci, a dukufa wajen neman dunkulewar jama'ar kasa da kasa domin bada tallafi ga mutanen kasa da kasa.
Na biyu, yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban zai ba da tabbacin neman ci gaba cikin hadin gwiwa. A halin yanzu, kasar Sin ta dukufa wajen aiwatar da shirin "Ziri daya da Hanya daya", inda ta bukaci kasa da kasa da su kiyaye tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, ta yadda za a kafa wani tsarin tattalin arziki wanda zai bude kofa ga waje cikin hadin gwiwa.
Na uku, ya kamata a goyi bayan kasashe mafi fama da talauci bisa dukkan fannoni domin za su shiga kungiyar WTO, kasar Sin tana maraba da kasashe masu fama da talauci da su shiga cikin kungiyar, ta kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su goyon musu baya.
A karshe, ya ce, kasar Sin tana son ba da taimako ga kasashe mafi fama da talauci. A watan Nuwambar shekarar 2018, kasar Sin za ta yi bikin baje kolin kayayyakin da kasar Sin ta shigar da su daga ketare karo na farko a birnin Shanghai. A lokacin, kasar Sin za ta ba da taimako ga kasashe mafi fama da talauci yadda ya kamata, domin yi musu maraba da halartar bikin. (Maryam)