Jiya Litinin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya sanar da cewa, bisa gayyatar da ministan harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson ya yi masa, wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jami'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana wakilin majalisar gudanarwar kasar ta Sin Yang Jiechi, zai yi ziyarar aiki a kasar Amurka a ranekun 8 da 9 ga watan nan da muke ciki.
Haka kuma, ya ce, kasashen Sin da Amurka sun nuna aniyarsu wajen karfafa shawarwarin dake tsakaninsu bisa fannoni daban daban. A yayin ziyarar Yang Jiechi a kasar Amurka, zai yi tattaunawa da jami'an kasar game da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, da wasu batutuwan kasa da kasa dake janyo hankulan kasashen biyu. (Maryam)