Mai magana da yawaun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, kasar ta lashi takobin daukar matakan da suka dace don tabbatar da tsaron dukkan yankunanta bayan da Amurka ta tura jirgin ruwan yaki a cikin tekunan dake kewaye da tsibirin nan na Huangyan dake tekun kudancin kasar Sin.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Lu Kang, ya tabbatar da cewa, da yammacin ranar Laraba ne aka shigar da jirgin ruwan yakin Amurka samfurin USS Hopper har zuwa wurin da ke da nisan mil 12 da tsibirin ba tare da samun izini daga gwamnatin kasar Sin ba.
A cewar Lu, sojojin ruwan kasar Sin sun gudanar da bincike gami da yin gargadi na neman a hanzarta kwashe jirgin ruwan yakin na Amurkar daga yankunan.
Kakakin ya ce, Abin da Amurkar ta yi, ya keta hurumin 'yancin mallaka da kuma tsaron kasar Sin, lamarin da zai iya yin barazana ga jiragen ruwan kasar Sin da sauran harkokin yau da kullum na kasar Sin a yankin.
Mista Lu ya ce matakin da Amurkar ta dauka ya saba muhimman ka'idojin kasa da kasa, kuma kasar Sin ta nuna rashin amincewarta da babbar murya.(Ahmad Fagam)