Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin na fatan Amurka za ta yi watsi da ra'ayin yakin cacar baki, ta kuma daidaita al'amuran kasa da kasa da huldar da ke tsakaninta da Sin yadda ya kamata.
Madam Hua ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani game da zargin da ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta yiwa kasar Sin cikin rahotonta game da manufofin tsaron kasa na shekarar 2018.
Rahotanni na cewa, a cikin rahotonta game da manufofin tsaron kasa na shekarar 2018, Amurka ta soki kasar Sin a fannoni da dama, a ganinta, manufar kasar Sin a nan gaba ita ce maye gurbin Amurka a fannin jagorantar duniya. (Tasallah Yuan)