in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ki yarda da rahoton da kasar Amurka ta gabatar dangane da batun nukiliya
2018-02-04 13:42:13 cri
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin, Ren Guoqiang, ya fada a yau Lahadi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin cewa, gwamnatin Sin ta ki yarda da wani rahoton da gwamnatin kasar Amurka ta gabatar dangane da batun nukiliya.

A cewar jami'in kasar Sin, cikin rahotonta, kasar Amurka ta yi shaci-fadi kan burin kasar Sin a fannin raya kasa, kana ta shafawa kasar Sin kashin kaji game da cewa yadda kasar ta mallaki makaman nukiliya barazana ce ga Amurka. Dangane da furucin kasar Amurka, jami'in ya ce, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufarta na samun cigaba cikin zaman lafiya, kana kasar tana tsara manufarta na harkokin soja ne bisa buri daya, wato don kare kai.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China