Kakakin ya bayyana cewa, a halin yanzu, kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa su ne muhimmin aiki a duniya, kana su ne burin zamantakewar al'ummar duniya baki daya. Idan wasu suna da ra'ayoyin yin yakin cacar baki da kyale zaman lafiya, za su maida dukkan duniya mai cike da yin gasa da takara da juna.
Kasar Sin kasa ce da ta taimaka wajen shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa da tabbatar da doka da oda a duniya. Sin tana bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da tsayawa tsayin daka kan manufar bude kofa ga kasashen waje da samun moriyar juna. Sin tana kokarin raya dangantakar abokantaka a tsakaninta da sauran kasashen duniya, bata neman iko ko mulki na kama karya na duniya. Kasa da kasa suna maraba da gudanar da ayyukan tattalin arziki da diplomasiyya da Sin ta yi wurare daban daban.
Kakakin ya kara da cewa, kasashen Sin da Amurka sun dauki alhakin tabbatar da zaman lafiya da na karko da samun bunkasuwa da wadata a duniya, suna da moriya iri daya a fannoni daban daban. Sin tana fatan kasar Amurka zata duba dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da ma duniya mai dacewa kamar yadda kasa da kasa da jama'arsu suke bukata, da yin kokari tare da kasar Sin, da tabbatar da bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata, ta haka za ta dace da moriyar jama'ar kasashen biyu har ma da jama'ar kasa da kasa a duniya baki daya. (Zainab)