Geng Shuang ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, rahoton ya yi kama da rahoton manufofin tsaro da rahoton dabarun tsaron kasa da kasar Amurka ta gabatar a kwanakin baya, wanda yake da ra'ayin yakin cacar baka dake tsakanin kasashe masu tsarin jari-hujja da masu bin tsarin gurguzu, da ra'ayin yin takara a tsakanin kasa da kasa wadanda yawan ribar da suka samu ta yi daidai da yawan hasarar da sauran kasashe suka tabka, da bayyana ra'ayin siyasa bisa yanayin wuri da yin takara a tsakanin manyan kasashe, da nanata rawar da makaman nukiliya ta taka yayin da ake aiwatar da manufofin tsaron kasa, da yin watsi da kiraye-kirayen da kasashen duniya suke yi game da rage makaman nukiliya. Ya ce wannan rahoto ya sabawa kokarin da ake na shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya.
Hakazalika, Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta shiga gasar makaman nukiliya ta ko wace irin fuska ba, da ci gaba da kiyaye yawan makaman nukiliya don bukatar tsaron kasar. Manufar kasar Sin kan wannan batu ba zai canja ba. (Zainab)