Yau Litinin ne madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin na fatan kasar Amurka za ta daidaita harkokinta da kasar Sin yadda ya kamata, tare da daukar hakikanin matakan kiyaye tsarin yin ciniki tsakanin sassa daban daban.
Madam Hua ta bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing.
A kwanan baya ne, gwamnatin Amurka ta mika wa majalisar dokokin kasar rahotonta na shekara-shekara, inda ta ce, yadda Amurka ta mara wa Sin baya wajen shiga kungiyar ciniki ta duniya wato WTO a shekarar 2001, kuskure ne. Ta kuma zargin kasar Sin da cewa, ta saba wa ka'idojin yin ciniki cikin 'yanci a duniya. (Tasallah Yuan)