A yayin ganawarsa da 'yan jarida bayan bikin rufe taron, Wang ya bayyana cewa, an gudanar da taron ministocin din a lokacin cikon shekaru 20 da kafuwar kungiyar WTO, kuma wannan shi ne karo na farko da aka gudanar da irin wannan taro a nahiyar Afirka. Bisa kokarin da sassa daban daban suka yi, an fidda wara sanarwar taron ministocin WTO, da kuma zartas da wasu kudurori a yayin wannan taro.
A cewa Mista Wang, an amince da shirin raya harkokin cinikin kasa da kasa cikin hadin gwiwa da adalci da kasar Sin ta fidda a yayin taron, wanda ya ba da gudummawa wajen cimma ra'ayi daya a yayin taron. Daga bisani kuma, an nuna yabo ga kasar Sin, domin babban taimakon da ta bayar wajen shigar da kasashe mafi fama da talauci cikin tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban daban. (Maryam)