Mr. Lamy ya bayyana haka ne a yayin dake ba da jawabi bisa taken "kawar da dunkulewar kasa da kasa ko sake dawo da dunkulewar kasa da kasa", yana mai cewa, shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21 yana kunshe da dabaru masu ma'ana. Ya ce bisa wannan shiri, kasar Sin tana habaka jarin da take zuba wa kasashen dake kan hanyar siliki, a fannin gina ababen more rayuwa, lamarin da ya dace da bunkatun kasashen. Sannan kuma kasashen suna maraba da kasar Sin kwarai da gaske.
Bugu da kari, ya ce bayan kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, ta yi ta bude kofa ga sauran kasashen waje, kuma a halin da ake ciki a yanzu, wasu kasashen duniya sun fara bin manufar kariyar ciniki bi da bi, sai dai a hannu guda, kasar Sin za ta kasance mai kiyaye zaman karko na bunkasuwar cinikayyar duniya. (Maryam)