A jawabinta na bude taro, shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf ta ce, amincewa da Liberiya ta zama mamba a WTO wani muhimmin al'amari ne mai dunbun tarihi, a daidai lokacin da kasar ke kokarin farfadowa bayan halin matsi da ta fada sakamakon bullar cutar Ebola a shekarar da ta gabata.
Liberiya ta kasance kasa ta 163 ciki jerin kasashe mambobin kungiyar WTO, kuma ita ce kasa ta 35 mafi koma baya ta fukar cigaba, cikin jerin kasashe mambobin kungiyar.
Sirleaf ta jaddada aniyar gwamnatin ta fuskar siyasa da tattalin arziki, wajen inganta sha'anin tattalin arzikin kasar.
Ana sa ran shigar Liberiyar cikin kungiyar WTO, zai janyo hankalin masu zuba jari a fannin tattalin arzikin kasar.
Shugaba Sirleaf ta ce, gwamnatin kasar ta tanadi kyakkyawan yanayi ga masu zuba jari a kasar a fannonin makamashi, da sufuri, da kayayyakin more rayuwa, da yawan bude ido da kuma harkar noma.
Babban daraktan kungiyar WTO Roberto Azevedo, ya bayyana cewa kasar Liberiya ta samu nasarar zama mamba a WTO ne, sakamakon irin rawar da take takawa a hulda da kasashen duniya.(Ahmad Fagam)