in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Kenya da Tanzaniya sun yi bikin bude wata hanyar mota da Sin da ta gina a Nairobi
2016-11-02 10:24:35 cri

Wata hanyar mota mai kewaye kudancin babban birnin Kenya, Nairobi, da kasar Sin ta gina, an yi bikin bude ta a ranar Talata a gaban idon shugaban Kenya Uhuru Kenyatta tare da takwaransa na Tanzaniya John Pombe Magufuli.

A yayin bikin, shugaba Kenyatta ya bayyana cewa, hanyar mai tsawon kilomita 28, dake hadewa manyan tagwayen hanyoyi, za ta taimaka cikin dogon lokaci wajen warware cunkuson motoci a Nairobi, da manyan motocin dakon kaya dake fitowa daga tashar ruwan Mombasa suke janyowa da kuma zuwa yammacin Kenya da babban bangaren gabashi da tsakiyar Afrika, in ji mista Kenyatta.

Shugaban Kenyan ya nuna cewa, layin hanyoyin motoci na zamani zai samar da karin alfanun tattalin arziki da na al'umma a Kenya da kuma dukkan shiyyar gabashin Afrika.

Hanyar dake kewaye kudancin Nairobi za ta kafa sabbin damammakin tattalin arziki a duk tsawon kan hanyar. Kuma za ta ingiza dunkulewar shiyyar bisa zirga-zirgar kayayyaki da jama'a cikin sauri, in ji mista Kenyatta.

Bankin Exim na Sin ya samar da kashi 85 cikin 100 na jarin da aka zuba domin gina hanyar kewaye kudancin Nairobi. Kamfanin gine-ginen hanyoyi da gadoji na kasar Sin ya gudanar da aikin gina hanyar, kuma a yanzu haka yana cikin aikin gina layin dogo na zamani a Kenya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China