Shugaba Kenyatta wanda ya ce gwamnatin sa ce ta daya waje yaki da cin hanci da rashawa, idan aka kwatanta da sauran gwamnatocin da suka gabata, tun samun 'yancin kai ya zuwa wannan lokaci, ya kara da cewa gwamnatin ta gurfanar da manyan jami'an hukuma da dama, wadanda suka aikata wadannan laifuka, a gaban kuliya.
Shugaban na Kenya wanda ke wannan kalamai yayin wani taron karawa juna sani a birnin Nairobi, ya ce matsalar cin hanci da rashawa, na cikin abubuwan da ke ci masa tuwo a kwarya. Daga nan sai shugaba Kenyatta ya bukaci al'ummar kasar da su raba cin hanci da batun siyasa, yana mai cewa akwai bukatar kotuna su kara azama, wajen kammala shari'un da ke da nasaba da cin hanci da aikata almundahana.(Saminu Alhassan)