Shugaba Omar al-Bashir na Sudan da takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta, sun alkawarta hakan ne a jiya Lahadi, yayin wani taron mane ma labarai na hadin gwiwa da suka gudanar a birnin Khartoum fadar mulkin kasar Sudan, lokacin da shugaban kasar Kenya ke kammala ziyarar aiki ta yini biyu da ya gudanar a Sudan.
An dai rawaito shugaba Al-Bashir na cewa ziyarar da shugaba Kenyatta ya gudanar a kasar sa, za ta bada damar bunkasa kawancen dake tsakanin kasashen a fannoni da dama. Ya kuma jinjinawa irin goyon baya da Kenya ke baiwa kasar sa, yana mai cewa zai ci gaba da martaba abotar dake wanzuwa tsakanin Sudan da Kenya, musamman a dukkan fannonin da za su amfani sassan biyu.
A nasa bangare kuwa, shugaba Kenyatta ya ce ya tattauna da shugaban kasar Sudan, kan batutuwan da suka jibanci shiyyar su, wadanda ke da nasaba da inganta sha'anin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kuma sun rattaba hannu kan yarjejeniyar bunkasa masana'antun su.
A daya bangaren kuma, takardar bayan taron da aka fitar bayan kammala ziyarar, ta nanata muhimmancin dake akwai na ganin an cimma nasarar warware matsalar siyasar da ta dabaibaye kasar Sudan ta Kudu.(Saminu Alhassan)