A jimilce, zuwa ranar 15 ga watan Oktoba, 'yan gudun hijirar Somliya dubu 33 da 178 suka koma kasarsu bisa son ransu tun daga ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2014, wato ranar da hukumar HCR ta fara bada kwarin gwiwa ga komawarsu gida bisa son rai, wanda kusan dubu 27 da 77 a shekarar 2016 kawai, in ji hukumar MDD a cikin wani rahoto.
Rahoton ya jaddada cewa 'yan gudun hijira 517 an kwashe ta jirgin sama a wadannan makwanni biyu na baya baya, tare da bayyana cewa an sake bude jigila ta hanyar jiragen sama zuwa sau uku a kowane mako.
Bisa dalilin dakatar da karbar ayarin motoci daga bangaren hukumomin Jubaland dake kudancin Somaliya, ayyukan sun fara saukaka dawowa zuwa Baidoa ta hanyar jirgin sama, in ji HCR.
A cewar MDD, wadannan ayarin motoci an dakatar dasu tun a ranar 30 ga watan Agustan da ya gabata bayan da hukumomin wannan yanki mai cin gashin kansa mai iyaka da Kenya suka sanar da HCR cewa ba za su amincewa da wadannan ayyukan dawowar 'yan gudun hijira ba idan har ba za a warware batun shirin dunkulewa a Somaliya ba. (Maman Ada)