Amma duk da haka ya bayyana cewa matsalar tsaron abinci ta kyautatu, inda ya kara da cewa yawan mutanen da suka yi fama da fari ya ragu, daga miliyan 2.5 a shekarar bara zuwa miliyan 1.3 a wannan shekara.
Jihohi takwas ne suka fi fama da matsalar fari, inda mazauna wuraren suke tsananin bukatar taimakon abinci na gaggawa da kuma kudade.
Mista Kiunjuri ya sanar da cewa, domin rage kaifin mugun sakamakon fari, baitulmalin kasa ya kebe dalar Amurka miliyan 2.5 a cikin watan Augusta domin saye da rabon abinci. (Maman Ada)