Loise Njoki, tana hannun hukumomin wannan yanki mai cin gashin kansa kafin a mayar da ita zuwa Kenya.
Andrew Mwangura, jami'in gudanarwa na ayyukan teku na gabashin Afrika, ya bayyana cewa aikin ceton sojojin musammun ya gudana cikin nasara.
Ana binciken lafiyar jikinta a halinzu kuma za a mayar Kenya domin saduwa iyalenta, in ji mista Mwangura.
An sace Loise Njoki tare da James Kuria a yayin da suke kokarin kai magunguna a Mogadiscio. Jami'an tsaron Somaliya sun ceto mista Kuria a cikin watan Febrairun shekarar 2015.
Saidai kuma har yanzu ba a da labarin wasu 'yan kasar Kenya biyu da mayakan na Somaliya suka sace a shekarar 2014, George Macharia Mburu da George Macharia Njoki. Mutanen biyu suna wa wani kamfanin gine gine (BTP) na Kenya dake Mogadiscio aiki a lokacin da aka kama su a yankin Habargidir na Somaliland dake arewaci.
Haka kuma wani na daban dan Kenya, Patrick Amukhuna, har yanzu yana hannun 'yan fashin teku tun lokacin da suka sace shi a shekarar 2008. (Maman Ada)