A jiya Laraba ne aka kaddamar da aikin gina layin dogo da zai hada biranen Nairobi da Malaba na kasar Kenya, aikin da kamfanin kasar Sin China Communications Construction (CCC) zai gudanar da shi. Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya halarci bikin kaddamar da aiki, inda kuma ya sanar da bude aikin a hukunce.
An ce, bayan kammala layin dogon, zai hada layin Mombasa zuwa Nairobi da layin jirgin kasa dake cikin kasar Uganda, ta yadda za a samu damar rage kudin da ake kashewa wajen jigilar kayayyaki tsakanin sassan shiyyar dake gabashin Afirka. (Bello Wang)