Mr. Baciro Dja ya bayyana cewa, gwamnatin kasar tana nuna goyon baya ga Sin da sauran kasashen da abin ya shafa da su daidaita matsalar yankin kasa da na teku ta hanyar yin shawarwari cikin lumana bisa yarjejeniya da kuma matsaya da suka cimma. Ya ce, a matsayin aminiyar kasar Sin, kasar Guinea-Bissau za ta tsaya tsayin daka kan nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Sin da jama'arta.
A nasa bangare, Wang Hua ya taya Baciro Dja murnar hawa kujerar firaministan kasar Guinea-Bissau. Yana fata baya ga zurfafa hadin gwiwa a fannonin aikin gona da aikin su da ma sauran fannoni tsakanin kasashen biyu, za a kuma fadada fannonin hadin gwiwa tsakaninsu, domin sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar kasashen biyu, tare da kawo alheri ga jama'arsu.(Fatima)