Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ziyarci aikin ginin layin dogo, wanda kasar Sin ke tallafawa wajen gina shi. Yayin wannan ziyara wadda ita ce ta biyu bayan watanni hudu, shubaga Kenyatta ya yaba da yadda aikin ke gudana.
Wannan layin dogo dai mai tsawo kilomita 472, an fara ginin sa ne a ranar 1 ga watan Jarairun shekarar bana, kuma zai kasance sabuwar hanyar jiragen kasa ta farko ga kasar cikin shekaru 100 da suka gabata. Ana kuma gudanar da aiki ne bisa ma'aunin fasahar kasar Sin. Idan kuma aka kammala shi, zai hade sassan birnin Mombasa na kasar ta Kenya.
Har wa yau shugaban na Kenya ya kira taron tattaunawa game da yadda aikin gina wata babbar gada dake kasar ke gudana, domin saurare rahoton aikin, da nufin sa kaimi ga warware matsalolin da ake fuskanta a aiki.
Da yake karin haske game da yanayin da ake ciki a aikin ginin layin dogon na Kenya, babban manajan kamfanin ginin sa ya ce yawan mutanen da kamfanin ya dauka aiki ya kai fiye da mutum dubu 10. Kuma masu aikin kimiyya da fasaha Sinawa kimanin 1900 na hadin gwiwa da wadannan ma'aikata 'yan kasa. Matakin da zai ba da damar horaswa ga ma'aikatan kasar ta Kenya.
Dadin dadawa, mutane fiye da dubu 30 za su samu guraben aikin yi bayan kammalar wannan aiki, kana GDPn kasar zai karu da kashi 1.5 bisa dari. Kazalika lokacin zirga-zirga daga Mombasa zuwa birnin Nairobin kasar ta Kenya zai ragu zuwa sa'o'i 4.
Bugu da kari aikin zai hade kasashen Kenya, da Uganda, da Ruwanda da Sudan ta kudu da dai sauran kasashen dake yankin. (Amina)