A kasar Kenya majami'un garin Garissa da kewayensa, sun tsaurara matakan tsaro biyowa bayan harin da kungiyar Al-Shabaab ta kaiwa jami'ar Moi dake garin a ranar Alhamis din makon jiya.
Rahotanni sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro kwarai a lokutan addu'o'in da suka gabata a jiya Lahadi, bayan aukuwar wancan hari da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 148. Wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya rawaito cewa an girke a kalla jami'an tsaro 3 zuwa 6 a daukacin majami'u 36 dake garin Garissa.
A daya hannun kuma majami'un da a baya ke cika da mutane, a wannan karo sun samu karancin masu halartar abada, sakamakon tsoron abinda ka je ya zo. An bayyana cewa da dama daga mabiya addinin kirista a Garissa sun kasance a gidajen su, inda suke ci gaba da tattaunawa game da tasirin wancan hari, wanda ya zamo mafi muni a tarihin yankin. (Saminu)