Rundunar ta ce, hare-haren na ranar Lahadi da Litinin da suka kunshi jefa boma-bomai a sansanonin kungiyar guda biyu sun lalata sansanonin gaba daya.
Kaza lika kakakin rundunar sojan kasar ta Kenya ya bayyana cewa, ko da yake ba a sami labarin adadin rasuwa da jikkatar 'ya'yan kungiyar ba, duk da haka akwai tabbacin wasu daga dakarun kungiyar sun rasa rayukan su sakamakon hare-haren.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai mayakan kungiyar ta Al-Shabaab suka kaddamar da wani hari cikin jami'ar Moi dake birnin Garisa, a arewa maso gabashin kasar Kenya, harin da ya haddasa mutuwar mutane 148, ciki hadda dalibai 142, da 'yan sanda 3, da kuma sojoji guda 3.
Kaza lika 'yan sandan kasar sun harba dakarun kungiyar su 4, lokacin da suke dauki-ba-dadi da mayakan, a kokarin ceto ragowar daliban dake cikin jami'ar.
Wannan dai hari na mayakan kungiyar Al-Shabaab ya zamo mafi muni, tun bayan da Kenyan ta fara tura sojojinta zuwa Somaliya, domin yaki da dakarun kungiyar ta Al-Shabaab a shekarar 2011. (Maryam)