in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tattaki mutane sama da 100 a jami'ar Nairobi ta Kenya
2015-04-13 09:39:48 cri

A jiya Lahadi 12 ga wata, rahotanni sun tabbatar da cewa,an shiga wani halin tashin hankalin da aka tattake mutane a Kikuyun a jami'ar Nairobi ta kasar Kenya, ya zuwa yanzu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane guda, tare da jikkatar wasu 141.

Bisa labarin da mataimakin shugaban jami'ar Peter Mbithi ya bayar, an ce, a sanyin safiyar ranar misali karfe 4 ne, injin din awon karfin wuta wato transforma ya fashe a yankin na Kikuyu na jami'ar dake karkarar yammacin Nairobi, abin da ya sa dalibai suka yi zaton ko wani harin 'yan ta'adda ne a jami'ar, suka fara rige-rigen tserewa, lamarin da ya sa aka samu tirmitsitsin da tattake mutane a wurin.
Bangaren 'yan sanda ya ce, dalibai da dama sun yi kuskure don ganin bom din ya zama harin ta'addanci, kuma wasu daga cikinsu ba su tsere a wurin fita ba, kawai suka rika tsalle daga ginin, har ma akwai wasu da suka yi tsalle daga dakinsu a bene na 6. Ya zuwa yanzu dai, dalibi daya aka tabbatar da mutuwarsa.

A ranar 2 ga wata, kungiyar Al-shabaab ta kai farmaki a jami'ar Moi dake birnin Garissa a yankin arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 148, cikinsu har da wasu dalibai 142.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China