Sufeto janar din 'yan sanda, Joseph Boinet ya bayyana cewa wadannan mutane da ake zargi da hannu a cikin ayyukan kungiyar Al- Shabaab zasu bayyana gaban cibiyar samar da bayanai kan yaki da ta'addanci domin su kare kansu da alaka da wadannan kungiyoyi.
Cibiyar samar da bayanai ta kasa kan yaki da ta'addanci nada sansaninta a birnin Nairobi, kuma mutanen da ake zargi da hada kai da kungiyar Al-Shabaab zasu bayyana domin suna nuna cewa basu cikin mutanen da ake zargi, in ji mista Boinet.
An fitar da wannan takardar jerin sunayen mutane bayan harin ta'addancin garin Garissa dake arewa maso gabashin Kenya, inda mayakan kungiyar Al-Shabaab suka kashe mutane 148.
Gwamantin Kenya ta sanya kungiyar Al-Shabaab a cikin jerin kungiyoyin ta'addanci, daidai da Boko Haram, Kungiyar IS da sauransu.
Haka kuma, Kenya ta dakartar da lasin wasu kamfanonin aiken kudi goma sha uku da take zarginsu da tallafawa ta'addanci. (Maman Ada)