Bisa hakan ne jama'ar kasar Kenya fiye da 100 suka taru a wani dandali dake birnin Nairobi, domin ban kwana, da alhinin wadanda wancan hari ya ritsa da rayukan su.
Jama'ar dauke da kyandira da furanni na cike da alhini, lokacin da suke tsaitsaye a wannan dandali, inda aka ajiye kuros 148, dake alamta yawan mutanen da suka rasu. Jama'ar da suka taru sun dora tutar kasar ta Kenya a kan wadannan kuros, tare da ajiye kyandira da furare a kewayensu don nuna jujayi.
Yayin da ake gudanar da bikin ta'aziyyar, jama'a sun rika rera wakokin kasar ta Kenya, tare da bayyana kudurinsu na hada kai don yaki da ta'addanci.
A ranar Alhamis din makon jiya ne dai mayakan kungiyar Al-Shabaab suka aukawa jami'ar Moi dake birnin Garissa, a arewa maso gabashin kasar ta Kenya, inda suka bude wuta kan daliban dake ciki, lamarin da ya haddasa mutuwar mutanen 148, tare da jikkata wasu da dama. (Zainab)