Shugaba Kenyatta ya yi jawabi ta gidan talebijin kasar cewa, Kenya na zaman makoki ga mutane 148 da suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai wa jami'ar Moi ta birnin Garissa, kuma ya yi alkawarin cewa, gwamnatin kasar za ta ba da taimako ga iyalan da lamarin ya shafa ta kowace hanya. Ya ce, gwamnatin za ta yi iyakacin kokarin gurfanar da duk wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya, tare da wadanda suka shirya harin Garissa.
Bayan haka, shugaba Kenyatta ya kara da cewa, ta'addanci na kasancewa babbar barazana ga kasashen duniya baki daya. A sabili da haka, dole ne gwamnatocin kasa da kasa su kara hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci.(Fatima)