Rahotanni daga ma'aikatar harkokin kudin kasa ta Sin sun nuna cewa, ya zuwa yanzu, jimillar kasashe 57 daga manyan nahiyoyin duniya biyar suka kasance cikin wannan tsari na kafuwar bankin, kana 37 daga cikinsu kasashe ne na nahiyar Asiya, yayin da 20 suka kasance daga sauran nahiyoyin duniya.
Bugu da kari, shugaban taron manyan wakilai a yayin shawarwari game da kafuwar bankin na AIIB, kana mataimakin ministan harkokin kudin kasa ta Sin Shi Yaobin, ya bayyana cewa bankin AIIB, zai bunkasa harkokin ci gaba ta hanyar hadin kan bangarori daban daban.
Ya ce ko da yake an riga an kawo karshen karbar takardar neman izinin shiga tsarin bankin, a hannu guda za a ci gaba da shigar da sabbin kasashe a nan gaba. Kana cikin shawarwarin da za a gudanar tsakanin mambobin bankin, hadda tattauna batun shiri, da manufofin shigar da sabbin mambobi. (Maryam)