Dangane da rahotannin da ke cewa kasar Sin ta yi watsi da ikon hawan kujerar-na-ki a bankin nan na zuba jari kan ababen more rayuwa na Asiya(AIIB) don samun karin goyon baya, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying a ranar laraban nan ta bayyana cewa, Sin tana tattaunawa ne da sauran mambobin bankin kan tsarinsa.
A bayanin da tayi ma manema labarai a nan birnin Beijing, Madam Hua ta ce hannun jarin da ko wace mambar ke da shi zai ragu muddin yawan mambobin ya karu. Dangane da rahotannin dake cewa kasar tana nema ko kuma ta yi watsi da ikon hawa kujerar na ki babu tushe ko kadan.
Ban da haka kuma, Madam Hua ta jaddada cewa, bankin AIIB na rike da ka'idar kawo moriyar juna cikin hadin kai, wanda zai ba da taimako ga tsarin tattalin arziki na kasa da kasa, kuma za a kafa ta bisa adalci ba tare da rufa rufa ba. (Amina)