Dangane da labaran da wasu kafofin yada labaru suka bayar na cewa, kasar Amurka ba ta iya hana wasu kasashen yammacin duniya niyyar shiga bankin saka jari game da muhimman ababen more rayuwa a Asiya wato AIIB ba, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Laraba a nan Beijing cewa, makasudin kafa bankin na AIIB shi ne kara azama kan bunkasuwar nahiyar Asiya da kawo wa jama'ar Asiya alheri. Kana bisa ka'idar kofar bankin a bude take ga kowa yayin da ake tafiyar da shi, hakan taimaka wajen kyautata yadda ake tafiyar da harkokin kudi a duniya. (Tasallah Yuan)