A ranar 18 ga wata, kasar Luxembourg ta sanar da neman shiga bankin zuba jari ga ayyukan more rayuwa na Asiya wato AIIB a matsayin kasa memba ta bankin, kana ta riga ta gabatar da takardar tabbatar da niyyarta ta neman shiga bankin ga kasar Sin. Game da batun, ma'aikatar harkokin kudi ta kasar Sin ta bayyana a daren ranar 19 ga wata cewa tana maraba da kudurin Luxembourg.
Ma'aikatar harkokin kudi ta kasar Sin ta bayyana cewa, a matsayin shugaban taron wakilan kasashe membobin da suka kafa bankin AIIB, kasar Sin tana sauraron ra'ayoyi daga kasashen da ke neman shiga bankin. Idan aka zartas da kudurin karbar Luxembourg, Luxembourg za ta kasance wata mamba daga cikin kasashen da suka kafa bankin AIIB a hukunce. (Zainab)