Ministan harkokin kudi na kasar Amurka Jacob J.Lew ya bayyana a jiya Talata cewa, kasar Amurka ta shirya sosai na yin maraba ga bankin zuba jari ga aikin gina manyan ayyukan yau da kullum na Asiya wato bankin AIIB wanda kasar Sin ta goyi bayan kafuwarsa.
Jacob J.Lew ya bayyana haka ne bayan da ya kammala ziyararsa ta kwanaki biyu a kasar Sin. Yana mai cewa, shugabannin kasar Sin sun mashi bayanin a yayin tattaunawarsu cewa, suna fatan bankin AIIB zai dace da ma'auni mai kyau, kuma suna son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya, abin da ya ba Mr. Jacob kwarin gwiwa sosai.
Jacob J.Lew ya ce, ya kamata kasar Sin da kasashe mafi ci gaban tattalin arziki na duniya su bayyana ra'ayoyinsu, kuma su kara taka muhimmiyar rawa wajen tsara ka'idojin tsarin kasa da kasa. Har ila yau ya jaddada cewa, kasar Amurka na maraba da kasar Sin wajen tsara tsarin tattalin arzikin duniya domin kasar Sin za ta kara daukar nauyi mai muhimmanci a yayin da take kara taka rawa a duniya.(Lami)