Kakakin Hong Lei ya bayyana hakan ne ga manema labarai a nan Birnin birnin Beijing lokacin da yake Karin karin haske akan tambayar cewa ko kasar nada aniyar hadin kai da Amurka wadda a baya ta yi kira ga kawayenta da kada su shiga bankin..
Mr Hong yace sauyin matsayi da Amurka keyi ya nuna cewa kudurin da bankin na AIIB ta dauka na samar da ababen more rayuwa a yankin Asia ya samu karbuwa.
A nashi bayanin shi ma Sakatare sakatare janar na ofishin wucin gadi mai kula da bankin AIIBsaka jari game da muhimman ababen more rayuwar kasashen Asiya, wato AIIB ,Ya ya ce Sin tayi tayin kafa wannan bankin ne domin ta cimma burin da yankin ke da shi na samar da ababen more rayuwa.
Gwamnatin Barrack Obama na Amurka ta yi tayin hadin gwiwwa tsakanin bankin na AIIB da sauran hukumomin kudi na duniya kamar su bankin duniya, kamar yadda jaridar wall street journal na Amurkan ta bayyana a jiya lahadi.
A yanzu haka dai bankin nada mambobi 27 da suka nuna sha'awar su na shiga cikin bankin. Haka kuma kasashen Birtaniya, Faransa, Jamus, Italiya, Luxembourg da Switzaerland su ma kwanan nan suka bukaci izni shiga cikin mambobin bankin.
Mr Jin yana sa ran adadin masu bukatar shiga ya karu zuwa 35 nan da karshen shekarar wannan wata da muke ciki lokacin da za'a rufe karban karbar takardun neman izini.