A wannan rana, yayin da mista Kim ke jawabi a cibiyar nazarin manyan tsare-tsare da muhimman batutuwan duniya ta kasar Amurka, ya bayyana cewa, bankin AIIB zai zama wani babban abokin hadin gwiwa ga bankin duniya wajen cimma burin rage talauci a duniya.
Ya ce, idan bankin AIIB da bankin raya kasashen BRICS da sauran hukumomin hada-hadar kudi na duniya suka kafa wani kawance a tsakaninsu, sun yi hada gwiwa don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, duk kasashen duniya za su samu moriya daga cikinsu, yana fatan wadannan sabbin hukumomi za su yi hadin gwiwa da bankin duniya don sa kaimi ga raya tattalin arziki, da rage talauci a duniya. Yanzu, akwai mutane kimanin biliyan guda da ke rayuwa da kudi kasa da dalar Amurka 1.25 a ko wace rana, kuma suna cikin kangin talauci.(Bako)