Wata sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce, jirgin mai lamba TM470 ya tashi ne daga birnin Maputo, hedkwatar kasar ta Mozambique da misalin karfe 11 da minti 26 na rana bisa agogon wurin, kuma har ya zuwa karfe 2 da minti 10 na yammacin ranar bai isa birnin Luanda, hedkwatar kasar Angola kamar yadda aka tsara ba. Har ila yau sanarwar ta ce, kawo yanzu ba a kai ga jin duriyar wannan jirgi ba, balle sanin halin da fasinjojin da ke cikinsa suke.
A cikin wannan jirgin saman fasinja, akwai fasinjoji 28 da ma'aikata 6. Kamfanin ya ce, ya zuwa yanzu ba a iya tabbatar da asalin wadannan fasinjoji ba
Dadin dadawa, sanarwar ta ce, an labarta ce, mai yiwuwa ne wannan jirgi ya sauka a yankin Rundu dake iyakar kasa tsakanin kasashen Namibia da Angola. Kamfanin ya ce, yana ci gaba da kokarin tabbatar da wannan hasashe.(Fatima)