Da sunan gwamnati, muna isar da ta'aziyya ga dukkan iyalan da wannan mummunan hadari ya rutsa da 'yan uwansu, tare da isar da godiya ga gwamnatocin kasashen Namibia, Bostwana da Angola kan kokarinsu na gano inda wannan jirgin sama ya fado, in ji mista Muthisse a yayin wani taron manema labarai a birnin Maputo.
Gwamnatin kasar Mozambique za ta sanar da zaman makokin kasa domin nuna alhini ga mutanen da suka mutu a wannan hadari bayan ta tattara bayanan da suka dace kan wannan lamari, in ji ministan.
Jirgin saman Mozambique dake dauke fasinjoji 27 da ma'aikatan jirgin 6 ya bace tun ranar Jumma'a, ya fado a Arewa maso Gabashin kasar Namibia, dukkan mutanen dake cikin wannan jirgi ba wanda ya tsirar da ransa a cewar jami'an 'yan sandan wurin a ranar Asabar. Jirgin dai na kan hanyarsa tsakanin Maputo da Luanda a yayin da wannan hadari ya abku, daga cikin wadanda suka mutu akwai dan kasar Sin guda, Bafaranshe guda, dan kasar Brazail guda, 'yan kasar Portugal 5, 'yan kasar Angola tara, 'yan kasar Mozambique goma da kuma ma'aikatan jirgin 6. (Maman Ada)