Rundunar 'yan sandan kasar ce ta tabbatar da hakan, tana mai cewa, an gano jirgin ne kirar kasar Brazil a arewa maso gabashin kasar Namibia.
Tun da fari dai kamfanin jiragen saman kasar ne ya sanar da batan jirgin, sakamakon zarta lokacin saukarsa da ya yi a filin tashi da saukar jiragen saman birnin Luanda na Angola, bayan ya bar birnin Maputo na kasar ta Mozambique a ranar Jumma'a da misalin karfe 9 da minti 26 agogon GMT.
Bayanan da kamfanin jiragen ya fitar a baya-bayan nan sun ce, cikin fasinjojin da suka rasa rayukansu sakamakon wannan hadari har da dan asalin kasar Sin daya, da yan kasar Mozambique su 10, da 'yan Angola 9. Sai kuma wasu 'yan asalin kasar Potugal su 5, da dan Faransa 1 da kuma dan kasar Brazil 1.(Saminu)