Bisa labarin da kafofin yada labarun yankin suka bayar, an ce, darurruwan matasa sun yi tururuwa kan tituna, don nuna adawa ga matakin da sojoji suka dauka na tilasa matasa shiga aikin soji. An ce hakan ne ya sanya sojoji shiga aikin kwantar da tarzoma, suka kuma rika harba bindiga da barkunon tsohuwa don tarwatsa gungun masu zanga zangar.
Sai dai a halin da ake ciki sojojin kasar sun musunta wannan labari, suna masu cewa sojoji ba su taba tilasa matasa shiga aiki ba, kuma lallai za a gurfanar da masu yada jita-jita gaban kuliya.
Wannan tarzoma dai ta auku ne bayan kidayar kuri'un zaben kananan hukumomin kasar, yayin da kuma ake nuna shakku ga sakamakon zaben wasu yankunan da hukumar zaben ta fitar, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a wasu biranen da ke yankin arewacin kasar. (Bako)